Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

[ad_1]


Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Nijeria (NCoS), reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa sauya wurin da ake tsare da malamin addinin Musulunci da ke fuskantar shari’a, Malam Abduljabbar Nasiru Kabara, zuwa wani gidan yari da ke karkashin ikon tarayya, hanya ce ta gudanar da aiki na yau da kullum wacce aka yi bisa ka’idojin da aka kafa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar a ranar Laraba a Kano.

A cewar sanarwar, an gudanar da sauya wurin ne bisa tanadin dokar Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Nijeria ta 2019, wacce ta bai wa hukumar ikon tafiyar da harkokin fursunoni yadda ya kamata a duk fadin cibiyoyin gyaran hali na kasar.

Sanarwar ta ce: “Sauya wurin da aka yi wa fursuna Malam Abduljabbar Nasiru Kabara zuwa daya daga cikin cibiyoyin tsarewa da ke karkashin ikon tarayya hanya ce ta gudanar da aiki ta yau da kullum wacce aka yi bisa ga dokokin aiki da ka’idojin hukumar.”

Ta kara da bayanin cewa motsa fursunoni daga cibiyar tsarewa zuwa wata musamman wadanda ke da matakan tsaro daban-daban na daga cikin ayyukan da kundin tsarin mulki ya dora wa hukumar domin tabbatar da ingantaccen tafiyar da fursunoni, gyarawa da kuma dawo da su kan turba.

Sanarwar ta kara da cewa: “Canjawa ko sauya wurin fursuna zuwa wata cibiyar gyaran hali mai matakin tsaro daban da wacce ake tsare da shi a baya na daga cikin ayyukan da kundin tsarin mulki ya ba Hukumar Kula da Gidajen Yari, kamar yadda Dokar Hukumar ta 2019 ta tanada.”

Sanarwar ta ce: “Ana yanke irin wadannan shawara ne bisa la’akari da abubuwa da dama, ciki har da tsaro, tsarin rarraba fursunoni, samun wurin da ya dace a cibiyoyi, da kuma bukatun gyarawa da farfado da fursuna.”

CSC Musbahu ya tabbatar wa jama’a cewa duk da wannan sauya wuri, ana ci gaba da kiyaye dukkan hakkokin Malam Abduljabbar.

Ya ce: “An tabbatar wa jama’a cewa walwala da dukkan hakkokin shari’a na Malam Abduljabbar suna nan daram karkashin kariyar doka.”

Sanarwar ta kara da cewa: “Wannan sauya wuri ba ya shafar matsayinsa na shari’a, hakkinsa na daukaka kara ko samun damar tuntubar lauyansa.”

Jami’in hulda da jama’a ya sake jaddada kudirin hukumar na tabbatar da tsare fursunoni cikin aminci, gyarawa da farfado da su, domin tabbatar da tsaron jiha da kare rayukan jama’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *