Duk da ce-ce-ku-ce sunan Maryam Sanda na cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
[ad_1]
Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa wasu wadanda suka hada da masu manyan laifuka kamar kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu.
A baya dai wasu sun yi ta suka da ce-ce-ku-ce kan sanya sunan Maryam Sanda cikin wadanda shugaba Tinubu ya yi wa afuwa.
Duk da maganganun mutane sunan Maryam Sanda na cikin sabon jerin sunayen wadanda aka bari, bayan cire wasu.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunan aƙalla mutum 50 daga tsohon jerin sunayen da aka fitar bayan ce-ce-ku-cen jama’a.
“Bayan martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen waɗanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, da fataucin mutane daga jerin waɗanda aka yi wa afuwa,” in ji Onanuga.
Ya ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne “don mutunta ra’ayoyin jama’a, inganta haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da al’umma baki ɗaya.”
Tsohon jerin sunayen da aka fitar ya haifar da cece-kuce a tsakanin jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.
Sun bayyana matakin a matsayin amfani da ikon shugaban ƙasa ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan barazana ce ga tsarin shari’a.
Sun yi gargaɗin cewa sakin waɗanda suka aikata manyan laifuka zai iya ƙarfafa aikata laifi da kuma rage wa doka tasiri.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link