Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe



Rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a Gundumar Komi, karamar Hukumar Funakaye ta Jihar Gombe, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane biyu, wasu da dama kuma sun jikkata, a cewar majiyar ‘yansanda.

Saɓanin ya fara ne a ranar Lahadi wanda daga bisani matasa daga al’ummomin makwabta suka hallara.

Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar Mohammed Jibrin, mai shekaru 27, dan shugaban gundumar Komi, wanda aka garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Biri da ke karamar hukumar Nafada bayan ya samu munanan raunuka, amma daga baya aka sanar da mutuwarsa.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, wasu manoma uku da makiyayi daya sun samu kananan raunuka. Ya kara da cewa an tura ‘yansanda da ‘yan banga na yankin don dawo da zaman lafiya.

Kakakin rundunar ‘yansandan ya kuma ce, sun kama mutane 17 da ake zargi da hannu a rikicin, amma zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a yankin.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *