Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya
[ad_1]
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida.
Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.
A cewar kwamitin, an tattauna kan buƙatu 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278.
Daga cikin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi shida; ɗaya daga kowanne yanki.
“Za mu binciki dukkanin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar domin gano inda za a fitar da sababbin jihohi shida.
“Za mu yi wa kowa adalc,” in ji ɗaya daga cikin mambobin kwamitin daga yankin Arewa Maso Yamma.
Idan Majalisar Tarayya ta amince da wannan yunƙuri gaba ɗaya, Najeriya za ta koma tana da jihohi 42 maimakon 36 da ake da su yanzu.
Wannan mataki, a cewar wani babban jami’in majalisar, “Yana nuna adalci da daidaito ga dukkanin yankuna,” kuma za a gabatar da rahoton kwamitin ga duka majalisun a farkon makon Nuwamba.
Sanata Barau, ya ce burin majalisar shi ne tabbatar da cewa duk wasu sauye-sauye da za a yi wa kundin tsarin mulki su kasance waɗanda za su amfani al’umma, tare da cika alƙawarin da aka ɗauka na tura sabon ƙudiri zuwa majalisun dokoki na jihohi kafin ƙarshen wannan shekara.
“Mun shafe sama da shekaru biyu muna taro da al’umma, ƙungiyoyi, da masana domin samun ra’ayoyi game da yadda za a inganta tsarin mulkin ƙasar nan,” in ji shi.
Taron na Legas ya kasance dama ga mambobin majalisar domin su nazarci sauye-sauyen da ake son yi, musamman batutuwan da suka shafi ƙirƙirar sabbin jihohi, daidaita iyakoki, da ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link