Ƙungiya ta tallafa wa ɗaliban makarantar masu buƙata ta musamman a Gombe
Ƙungiyar Arewa Unity Women in Media, ta kai tallafi Makarantar Masu Buƙata ta Musamman da ke Gombe, domin taimaka wa gwamnati wajen kula da rayuwar ɗaliban da ke da buƙata ta musamman.
Tallafin ya ƙunshi gidajen sauro, bargo da tabarmi, wanda aka raba wa ɗaliban a lokacin bikin miƙa kayan tallafin.
Shugabar ƙungiyar, Lois Hassan daga GMTV Gombe, tallafin na da nuna kulawa da ƙauna ga ɗaliban, tare da tabbatar musu cewa al’umma ba ta manta da su ba.
Ta ƙara da cewa ƙungiyar Arewa Unity Women in Media ƙungiya ce mai zaman kanta da ke gudanar da ayyukan jin-ƙai domin tallafa wa marasa galihu da ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma.
Malaman makarantar, Joy Samuel da Maimuna Manager, sun yaba da wannan tallafi, inda suka roƙi gwamnati ta samar da magunguna a cibiyar lafiya ta makarantar.
Haka kuma, sun buƙaci ƙungiyoyi da masu hannu da shuni su yi koyi da irin wannan aiki na alheri.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka amfana da tallafin, Comfort Ephraim da Barisasa David, sun bayyana farin cikinsu, inda suka bayyana cewa tallafin ya zo a lokacin da suke buƙata sosai.
Sun kuma roƙi gwamnati da ta gyara wutar lantarki a makarantar domin inganta tsaro da yanayin karatu.