Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja




Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja.

Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, sabon kwamishinan ya bayyana cewa zai ci gaba da inganta tsaro tare da bunkasa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’ummar Abuja.

Ta ce CP Miller ya yi alkawarin samar da tsari domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin mazauna Babban Birnin Tarayya.

Rundunar ta kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bai wa ’yan sanda hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Abuja.

Adeh, ta bayyana Dantawaye Miller a matsayin gogaggen jami’in tsaro da ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a wurare daban-daban a faɗin ƙasar nan.

An haife shi a ranar 15 ga watan Oktoban 1971, a ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, kuma ɗa ne ga marigayi DCP Gajere Dantawaye.

Ya shiga aikin dan sanda a watan Mayu, 2000, inda ya fara aikinsa a Jihar Bayelsa a shekarar 2002.

A tsawon lokacin da ya shafe yana aiki, Miller ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da mukamin babban mai tsaron tsohon gwamnan Bayelsa, kwamandan rakiyar tsohon mataimakin shugaban ƙasa.

Ragowar mukaman sun hada da jami’in tsaro na musamman a Ma’aikatar Man Fetur, da kwamandan MOPOL 24 da ke aiki a Fadar Shugaban Ƙasa.

Haka kuma, ya taɓa zama Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a Abuja, kwamandan yanki a Jihar Adamawa, Mataimakin Kwamishina a Jihohin Yobe da Edo, da Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Fasahar Sadarwa a hedikwatar rundunar.

Kafin yanzu, shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi.

A ’yan watannin nan, an samu ƙarin matsalolin tsaro a Abuja duk da ƙoƙarin da ’yan sanda ke yi na dakile su.

Saboda haka, ana sa ran sabon kwamishinan, CP Dantawaye, zai kawo sabbin dabaru da shugabanci domin inganta tsaro a Babban Birnin Tarayya, Abuja




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *