Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

[ad_1]



Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa.

Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu.

Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba.

An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa  da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin waɗanda ake zargin suna da hannu wajen tafka almundahana a tallafin man fetur.

Bayan ya kammala zaman gidan yari, an sake shi a watan Oktoban 2024.

Lawan, ya ce wannan ta sauya masa tunani game da siyasa da aminci.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Lawan, ya bayyana cewa tafiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da shi, duk da cewa ya dade yana cikin tafiyar.

“Idan Allah Ya jarabce ka, zai nuna maka waye na gaskiya a cikin abokanka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wani muhimmin jagora a tafiyar bai taɓa kira ko yi masa jaje ba lokacin da yake gidan yari ko bayan fitarsa.

“Yanzu shekara ɗaya kenan da fitowa ta, amma bai kira ni ba ko ya ce ‘Allah ya taimake ka ba’,” in ji Lawan.

Lawan ya bayyana cewa a lokacin da yake a gidan yari, ya umarci magoya bayansa su shiga jam’iyyar NNPP a lokacin zaɓen 2023.

Amma yanzu yana ganin jam’iyyar karama ce da burinsa na siyasa.

“Siyasa ya kamata ta zama mai faɗi, amma yanzu NNPP ta yi mini ƙarama,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanzu zai mayar da hankali kan siyasar ƙasa baki ɗaya, maimakon yin tafiya a waje guda.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *