Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF

[ad_1]



Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zuba jari a fannin kayan aikin wanke hannu da kuma ilimin tsafta.

Asusun ya kuma ce kaso 35 cikin 100 na makarantu ne kawai ke da kayan wanke hannu na asali, yayin da kashi 8 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke iya nuna yadda ake wanke hannu daidai.

Yayin wata ziyara da aka kai makarantu a Jihar Borno a ranar Laraba, a wani ɓangare na bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta shekarar 2025, Shugabar Ofishin UNICEF a Maiduguri, Dr. Marie Marcos, ta ce zuba jari a kayan wanke hannu zai ƙara adadin masu zuwa makaranta, inganta lafiyar al’umma, da kuma ƙara ƙwarewa a wuraren aiki.

A cewarta, yankin Arewa maso Gabas ne ke matsayi na biyu a Najeriya dangane da gidaje da ke da wuraren wanke hannu da ruwa da sabulu.

Marie ta ce, “Duk da cewa kaso 99 cikin 100 na ’yan Najeriya sun san lokacin da ya dace a wanke hannu, kashi 8 cikin 100 ne kawai ke iya nuna yadda ake wanke hannu daidai.

“Kaso 17 cikin 100 na gidaje ne ke da damar samun tsafta na asali. Kaso 35 cikin 100 na makarantu ne ke da kayan wanke hannu da ruwa da sabulu.”

“Arewa maso Gabas na matsayi na biyu a Najeriya dangane da gidaje da ke da wuraren wanke hannu da ruwa da sabulu, duk da cewa adadin ya yi kadan a matakin ƙasa baki ɗaya, wato kaso 22.1 cikin 100,” in ji ta.

Sai dai ta ce UNICEF, ta hannun Gwamnatin Jihar Borno, ta tallafa wajen kafa tsarin wanke hannu a makarantu 50 a faɗin jihar, wanda ke kare kusan ’yan makaranta 20,000 a halin yanzu.

“A Jihar Borno, kaso 14 cikin 100 na gidaje ne ke da kayan wanke hannu da sabulu da ruwa. Kashi 20 cikin 100 na makarantu ne ke da kayan tsafta na asali,” in ji ta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *