Masarautar Nafada ta ƙaddamar da dokar rage tsadar aure

[ad_1]



Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Dadum Hamza ya ƙaddamar da sabuwar doka ta rage tsadar aure a masarautarsa, a Jihar Gombe domin sauƙaƙa wa matasa yin aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin yin aure a cikin al’umma.

Wakilin Sarkin, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), ne ya gabatar da dokar yayin taron ƙaddamarwa da aka gudanar a Unguwar Madaki da ke Nafada ta Tsakiya, tare da halartar jami’an gwamnati, Alƙalan kotun majistare da jami’an tsaro.

Dokar za ta fara aiki daga wannan shekara ta 2025, inda aka gargaɗi matasa da su guji yin habaici ko izgili ga ma’aurata da kalmomin da ke nuna raini kamar: “Aure ya yi arha”. Duk wanda aka kama yana aikata hakan zai fuskanci hukunci.

Sarkin ya ce, matakin yana da nufin ƙarfafa tarbiyya, inganta zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma, tare da rage nauyin da iyaye da matasa ke ɗauka wajen yin aure.

Ya ƙara da cewa, manufar dokar ita ce dawo da aure ya zama da sauƙi kamar yadda addini ya tanada.

Mahalarta taron sun yaba da wannan mataki, suna mai cewa zai taimaka wajen rage zaman banza da matsalolin da ke addabar matasa da iyalai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *