Ban san yadda zan kashe N150m da na lashe ba — Imisi Eniola
[ad_1]
Gwarzuwar gasr Big Brother Naija (BBNaija) ta wannan shekara, Imisi Eniola Ayanwalwe, ta ce ba ta san yadda za ta kashe Naira miliyan 150 da ta lashe a gasar ba.
Imisi Eniola Ayanwale ce ta zama gwarzuwar BBNaija da aka kammala a daren Lahadi ne bayan kwanaki 70 ana fafatawa mai cike da ce-ce-ku-ce da nishaɗi.
An sanar da sakamakon tare da karrama ta da kyaututtuka ne a babban bikin ƙarshe da Ebuka Obi-Uchendu ya gabatar, inda Imisi ta doke abokiyar takararta Dede a karshe.
Ta tafi da tsabar kuɗi Naira miliyan 80 a matsayin wani ɓangare na kayatattun Naira miliyan 150 da ta lashe a matsayin gwarzuwar BBNaija karo na 10.
A bana, masu shirya gasar sun canja tsarin yadda ake fitar da zakara, inda suka ce za a zabi gwarzon ne daga cikin mutum 10 na ƙarshe da suka rage a gidan, maimakon mutum biyun ƙarshe kamar yadda aka saba. Amma daga bisani gasar ta dawo yadda aka saba, aka bar Imisi da Dede a zagayen ƙarshe kafin a sanar da sakamakon.
Bayan sanar da ita a matsayin zakara, Imisi ta bayyana farin ciki da godiya, tana mai cewa har yanzu bata tsara yadda za ta yi da kuɗin ba.
Ta ce, “A gaskiya ban shirya yadda zan yi da kuɗin ba tukuna. Zan fara neman shawarar kuɗi tukunna, domin ban taɓa rike irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba.”
A zamanta na ƙarshe da Big Brother kafin kammala gasar, Imisi ta bayyana cewa ta koyi darussa da dama yayin zamanta a gidan, ciki har da juriya da sanin kanta.
Imisi ta shahara saboda halayenta na raha, annashuwa da tsage gaskiya da kuma yadda take warware saɓani cikin natsuwa, abin da ya jawo mata masoya da dama a shafukan sada zumunta.
Kafin sanar da sakamakon, masu kallo sun zaƙu suna jiran wanda zai zama zakara a bana, wanda yanzu Imisi ta shiga jerin fitattun zakarun baya kamar su Phyna, Mercy Eke, Laycon, Whitemoney, da Ilebaye.
An rufe gasar ta BBNaija kaka ta S10 da shagulgula, inda Imisi ta bar dandali cikin farin ciki da kyaututtuka da kuma tarihi da ba za a manta da shi ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link