An gudanar da zangar-zangar goyon bayan Kwamishinan ’Yan Sanda a Kano




Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori.

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka kyale mana CP.”

Zanga-zangar na zuwa ne dai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya caccaki  Kwamishinan ’Yan Sandan kan ƙaurace wa farerin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata.

Yayin da yake jawabi a bikin da aka gudanar a filin wasa na Kofar Mata, gwamnan ya nuna ɓacin ransa kan abin da ya kira “halin rashin kishin ƙasa da kwamishinan ke nunawa a jihar.”

Gwamnan ya zargi kwamishinan da janye jami’an ’yan sanda daga filin taron a daidai lokacin da ake dab da farawa, inda ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya cire shi daga muƙamin.

Gwamnan ya ce, “A ƙarshen jawabina, ina kira ga dukkan hukumomin tsaro da su ci gaba da sadaukar da kansu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihohin ƙasar nan, ciki har da Kano.

“Amma musamman hukumomin tsaro a Kano, bai kamata su tsoma kansu cikin siyasar bangaranci ba, domin hakan ba zai amfani kowa ba a Kano da ma Najeriya ba.

“Ina so in yi amfani da wannan dama a matsayina na ɗan Najeriya, ɗan Kano, kuma Babban jami’in tsaron Jihar Kano, in yi Alla-wadai da halin rashin ƙwarewa da nuna bangaranci da Kwamishinan ’Yan Sanda na yanzu ke nunawa,” in ji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya ce rashin halartar Kwamishinan da jami’ansa a bikin wani mataki ne da aka yi da gangan, kuma ya ce hakan ya jawo wa jihar kunya a rana mai tarihi.

“Kamar yadda kuke gani, a wannan rana ta tarihi ta bikin ’yancin kai na Najeriya, ya yanke shawarar ya janye daga jerin faretin tare da jami’ansa.

“Wannan mataki ne da ya shafe shi da mutanensa. A matsayina na Babban Jami’in Tsaro na Kano, a madadin gwamnati, ba mu ji dadin wannan hali da Kwamishinan ’Yan Sanda ya nuna ba,” in ji shi.

Haka kuma, gwamnan ya ƙara da cewa zai rubuta ƙorafi a madadin gwamnati da al ummar Kano zuwa ga shugaban ƙasa ta hanyar ofishin bai ba shi shawara kan harkokin tsaro.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *