Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba
[ad_1]
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya.
Tunji-Ojo ya taya ’yan Najeriya da ke zaune a nan cikin gida da ƙetare murnar zagayowar wannan rana mai tarihi, kamar yadda babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana a ranar Litinin.
Ministan ya roƙi ’yan Nijeriya da su ci gaba da rungumar kishin ƙasa, haɗin kai da kuma juriya, domin a cewarsa, su ne ababen da ke riƙe da ƙasar tun daga samun ’yancin kai a shekarar 1960 zuwa yau.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link