2027: APC za ta ƙwace Kano ba tare da taimakon Kwankwaso ba – Jigon APC

[ad_1]



Jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Seyi Olorunsola, ya ce jam’iyyar za ta iya samun nasara a jihar a zaɓen 2027 ba tare da taimakon Rabiu Musa Kwankwaso ba.

A baya-bayan nan an yi ta raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai fice daga NNPP tare da komawa jam’iyyar APC.

A taron manema labarai da ya yi a Kano ranar Lahadi, Olorunsola, ya ce Shugaba Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, sun bai wa Kwankwaso kulawa fiye da ƙima.

Ya ce APC na da manyan ’yan siyasa a Kano da za su iya tabbatar da nasarar jam’iyyar.

Ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Atah, da Sanata Kawu Sumaila za su iya kayar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027.

A cewarsa, Atah, zai ƙalubalanci Gwamna Abba a Kano ta Tsakiya, yayin da Barau Jibrin da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje za su jagoranci Kano ta Arewa, sannan Kawu Sumaila ya kula da Kano ta Kudu.

Olorunsola, ya bayyana cewa ƙungiyarsu, wato Tinubu/Barau/Atah Movement, ta shirya tsayar da Barau Jibrin a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a 2027.

A gefe guda kuma, ya zargi Kwankwaso da yunƙurin shiga APC, domin karya shirinsu tare da bai wa Abba damar sake zama gwamna.

Ya kuma jaddada cewa APC ta lashe zaɓen gwamna na 2023, inda ta yi nasara a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe da kotun ɗaukaka ƙara, amma daga baya kotun ƙoli ta yanke hukunci akasin abin da yake na gaskiya.

Olorunsola, ya gargaɗi Shugaba Tinubu da kada ya dogara da Kwankwaso wajen samun nasara a Kano.

Ya ce Kwankwaso ba shi da wani cikakken iko a jam’iyyarsa ta NNPP.

Ya ce idan Kwankwaso na son shiga APC da gaske, dole ne ya fara daga matakin unguwa, Ƙaramar Hukumar da jiha tare da bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ƙa’idojinta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *