Mun haramta amfani da littattafai masu wa’adin amfani ɗaya —Gwamnatin Gombe
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe ta haramta amfani da littattafan karatu da ba sa iya amfani sau biyu da kuma bukukuwan ‘sign-out’ da dalibai ke gudanarwa a bayan jarrabawar kammala karatu.
Daraktan Kula da Ingancin Ilimi na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Sa’idu Dauda Gadam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.
Ya ce yin littattafai masu guraben amsoshi ko sarari na rubutu da ba sa sake amfani yana jefa iyaye cikin halin ƙuncin tattalin arziki, tare da haifar da asarar kuɗaɗe.
Don haka, daga ranar 15 ga Satumba, 2026, dukkan makarantu za su daina amfani da irin wadannan littattafai.
A maimakon haka, za a samar da littafi na koyarwa mai ɗorewa, sannan dalibai su riƙa amfani da takardun rubutu na daban don ɗaukar darussa da amsoshi.
Haka kuma, Gwamnati ta haramta bukukuwan sign-out da ake gudanarwa a makarantu, musamman a lokutan da ake samun munanan dabi’u da rashin tsaro daga dalibai.
Wannan al’ada, daliban da suka kammala aji shida na firamare da JSS 3 da SS 3 ne suke aikata ta, inda suke lalata kayan makaranta da faɗace-faɗace game da wasu abubuwa na fitsara.
Bugu da kari, Gwamnati ta dakatar da rijistar sababbin makarantu masu zaman kansu, na al’umma da na addini, har sai an kammala sake duba tsarin.
Duk makarantu da ba su kammala rijista ko karɓar takardar sahalewar aiki ba, an umarce su da su tabbatar sun gama kafin 31 ga Oktoba, 2025.
Sanarwar ta kara jaddada cewa dukkan makarantu masu zaman kansu su daidaita ayyukansu da manufofin gwamnati, ciki har da bin sabon manhajar NERDC, koyar da sana’o’i, da kuma aiwatar da manufofin yaƙi da cin zarafi da zaluncin ɗalibai.
Haka kuma duk manyan makarantu masu zaman kansu da ba su da cibiyar jarrabawar waje irin su WAEC, NECO, NABTEB ko NBAIS, an umurce su da su tuntubi Ma’aikatar Ilimi domin samun shawarwari.
Ma’aikatar ta jaddada aniyar gwamnatin jihar na tabbatar da ingantaccen ilimi mai araha, da kuma bai wa kowa damar samu a Jihar Gombe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link