Ƙasashen duniya sun ƙaurace wa Isra’ila a Babban Taron MƊD
[ad_1]
Wakilan ƙasaahen duniya sun ƙaurace wa jawabin Shugaban Ƙasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya domin su nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasɗinawa.
Fiye da rabin wakilan da suka halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) sun miƙe tare da ficewa daga zauren taron ne a yayin da Mista Netanyahu yake shirin gabatar da jawabin ƙasarsa ta Isra’ila.
Zauren taron ya kasance kusan wayan, in banda ’yan jarida da jami’an MƊD da wasu tsirarun wakilan ƙasashe da suka rage a ciki a lokacin jawabin Mista Netanyahu wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ba da umarnin kamo shi domin gurfanarwa kan laifukan yaƙi a Zirin Gaza inda dakarun Isra’ila suka kashe mutane kimanin 79,000, akasarinsu ƙananan yara da tsofaffi da kuma mata— baya ga jikkata wasu fiye da hakan.
Ƙauracewar ƙasashen domin nuna fushi ga Isra’ila ta faru ne a bayan ƙarin manyan ƙasashen duniya kuma ƙawayen Isra’ilar, irin su Faransa da Ingila da Kanada sun sanar da taron na MƊD game goyon bayansu ga batun kafa ƙasar Palasɗinu mai cikakkiyar ’yanci.
Hakan ta faru ne kwanaki kaɗan bayan rohoton kwamitin bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa kan mamaya da yaƙin da Isra’ila ta shafe shekara biyu tana yi a Gaza ya samu shugabanni da sojojin Isra’ila da laifin yi wa Falasɗinawa kisan ƙare dangi.
Baya ga kisan mutane kimanin 70,000 — wasunsu a asibitoci da makarantu da sansanonin ’yan gudun hijira da wuraren da Isra’ila ta ayyana a matsayin masu aminci a Gaza, jirage da tankokin yaƙin Isra’ila sun rushe gidajen sama da mutum miliyan ɗaya, baya ga wuraren ibada da makarantu da asibitoci da sauran wuraren taruwa jama’a.
Kazalika Isra’ila ta lalata abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da wutar lantarki da sufuri, haka kuma ta hana shigo da kayan agaji — na abinci da magunguna da sauransu — zuwa Gaza.
Netanyahu ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta dakatar da yaƙin ba har sai ta ƙwace Gaza ta murƙushe ƙungiyar Hamas sa’annan ta ƙwato ’yan ƙasarta da ƙungiyar ta yi garkuwa da su tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda Hamas ta kai mata harin ba zata, ta kashe mutane 1,200 tare da sace wasu kimanin 250.
Ƙasashe da dama sun la’anci ayyukan Isra’ila a Gaza, a rikicin da ya samo asali sama da shekaru 40 da suka wuce, kan mamaye ƙasar Palasɗinu da Isra’ila take yi, tana kafa wa Yahudawa matsugunan kama-wuri-zauna.
Tun lokaci mai tsawo, kasashe da hukumomin duniya sune ta nananta cewa kafa ƙasashe biyu — Palasɗinu mai ’yanci da kuma Isra’ila, a matsayin mafita ga rikicin wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link