Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance




Faransa ta bi sahun Birtaniya, Australia da Canada da sauran ƙasashen duniya sama da 140 da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ne ya tabbatar da amincewar gwamnatinsa na kafa ƙasar Falasɗinu a hukumance.

Macron ya bayar da tabbacin ne a yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Mista Macron ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da sakin sauran Isra’ilawa 48 da Hamas ke garkuwa da su.

Ya ce lokaci kaɗan ne ya rage wa duniya ta iya wanzar da zaman lafiya, don haka ya ce bai kamata a jira ba.

Mista Macron ya yi Allah-wadai da harin na ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai wa Isra’ila.

Shugaban na Faransa ya ce yana son ganin an samar da zaman lafiya a yankin ta hanyar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kai da ke zama makwabtan juna.

“Babu wata hujja na ci gaba da yaƙin Gaza”, in ji Macron, yana mai ƙarawa da cewa “ya kamata a kawo ƙarshen komai.”

A yau ne dai tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a birnin Landan, kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *