Ambaliya ta lalata gidaje da gonaki a Kaduna
[ad_1]
Mazauna garin Manchok a masarautar Moro’a, da ke Ƙaramar Hukumar Kaura, a Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta tarayya su kai musu ɗauki bayan ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a yankin.
Ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe kwana uku a jere ana yi.
Hakan ya janyo ambaliyar ta lalata gidaje, gonaki da amfanin gona.
Lamarin ya bar jama’a cikin firgici da tashin hankali.
Ɗaya daga cikin mazauna yankin, Duniya Awuwu Sambo, ya ce ruwan ta shigar masa gida inda ya lalata masa dukkanin kayayyakinsa.
Ya ce shi da iyalinsa sun kwana suna kwashe ruwa daga cikin ɗakin da suke kwana.
Wani manomi, Luka Ishaya, ya bayyana cewa duk amfanin gonarsa ya lalace, wanda shi ne kawai hanyar samun rufin asirinsa.
Hakazalika, wani mazaunin yankin, Thomas Yatai, ya danganta matsalar da toshewar hanyoyin ruwa da kuma rashin magudanai masu kyau.
Ya ƙara da cewa rashin wuraren zubar da shara ya sa jama’a ke zubar da ita a kan tituna da cikin magudanai.
Shugaban matasan Manchok, Moses Mathew, ya ce matasa sun fara sharar magudanai na wucin gadi da share hanyoyin da suka toshe, yayin da suke jiran agajin gwamnati.
Ko da yake babu wanda ya rasa ransa, mazauna yankin na ci gaba da fargabar irin ruwan saman da za a samu daga Satumba zuwa ƙarshen Oktoba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link