Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II
[ad_1]
Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan a ranar Litinin.
Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta a cikin cocin St. George’s Chapel da ke fadar Windsor.
Mai magana da yawunsa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Harry ya kai ziyara shi kaɗai domin girmama mahaifiyarsa.
A halin yanzu dai abin tambayar shi ne ko Yarima Harry zai gana da mahaifinsa, Sarki Charles III, wanda ke fama da cutar daji, bayan shekaru suna fama da rigimar cikin gida.
Rabon Harry ya gana da mahaifinsa tun watan Fabrairu 2024, lokacin da ya yi gaggawar dawowa Ingila bayan ya samu labarin cewa sarkin mai shekara 76 na fama da jinya.
Yarima Harry, mai shekara 40, ya halarci bikin ba da kyaututtuka na WellChild a daren Litinin a birnin London, inda ake girmama jarirai da yaran da suka yi bajinta duk da nakasa ko rashin lafiya.



Bayan haka kuma, ana sa ran zai tafi Nottingham a Arewacin Ingila a ranar Talata domin ziyartar wani gidan rikodin al’umma da kuma sanar da tallafin kuɗi a shirin Children in Need, wata ƙungiya da ke fafutukar taimaka wa yaran da ke cikin mawuyacin hali.
Tun daga shekarar 2020 Harry ya daina shiga harkokin gidan sarauta kai tsaye, lamarin da ya jawo cece-kuce, musamman tsakaninsa da ɗan uwansa Yarima William, wanda shi ne mai jiran gado.
A watan Mayu, Yarima Harry ya bayyana cewa yana fatan a samu sulhu tsakaninsa da ’yan uwansa, yana mai cewa: “Ban san adadin kwanakin da suka rage wa mahaifina a duniya ba.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link