Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, biyar ga watan Satumban 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
Ana dai yin bikin ranar ce dai da ake kira ta Mauludi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wat ana uku a shekarar Musulunci.
Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, ranar Laraba a madadin gwamnatin, kamar yadda Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta sanar.
Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya murna, inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Annabin na zaman lafiya, kaunar jama’a, hakuri, tawali’u da kuma tausayi.
Tunji ya kuma yi kira ga dukkan ’yan kasar ba tare da la’akari da kowanne irin addini suke bi ba da su yi amfani da lokacin Mauludin wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da tsaro tare da goyon bayan yunkurin gwamnati na bunkasa rayuwarsu.
“Ministan Harkokin Cikin Gida yana kuma yi wa ’yan Najeriya fatan yin shagulgula cikin farin cikin, natsuwa da kwanciyar hankali,” in jin sanarwar.