Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau

[ad_1]



Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya.

A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce za a karrama Sarkin tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda shida a babban taron shekara-shekara da cibiyar ke shiryawa.

Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, a Cibiyar Karatun Alƙur’ani da Addinin Musulunci ta Sultan Muhammadu Maccido da ke Sakkwato.

Cibiyar ta ce kakan Sarkin Zazzau na yanzu, Malam Musa Kaka, na cikin dakarun da suka taka muhimmiyar rawa a yaƙin Tafkin Kwato, wanda aka fi sani da Muhajiruna wal-Ansar, yaƙin da ya taimaka wajen ginawa da kuma ƙarfafa Daular Usmaniyya.

Ana sa ran fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Talatan Mafara, zai gabatar da kasida mai taken: “Muhajiruna wal-Ansar: Kafuwar Gidajensu wajen Haɓaka Daular Usmaniyya.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *