’Yan sanda sun ceto yara 3 da aka sace a Kaduna
[ad_1]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ta ceto wasu yara guda uku da aka sace tare da kama mutum uku da ake zargi da sace su.
A ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025, wani mutum ya kai rahoton cewa an sace ’ya’yansa uku.
Yaran sun haɗa da Aslam Umar Lukman mai shekaru 14, Suleiman Umar Tanko mai shekaru 12 da Aliyu Umar Tanko mai shekaru 10.
Waɗanda suka sace yaran sun nemi a ba su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.
’Yan sanda sun yi amfani da dabaru inda suka cafke shugaban ƙungiyar, Richard Philip.
Yayin bincike, ya amsa laifin tare da bayyana sunayen waɗanda suka taimaka masa; Ibrahim Ma’aruf mai shekaru 18 da Abubakar Sadiq mai shekaru 15.
Daga baya ’yan sanda sun kai samame maɓoyarsu, tare da kama sauran sannan suka ceto yaran ba tare da wata matsala ba.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya damƙa yaran ga iyayensu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link