An Gudanar Da Ayyukan Share Kaburbura A Fadin Kasar Sin A Rana Ta Biyu Ta Hutun Qingming
[ad_1]
Yau Lahadi ce kuma ranar bikin Qingming ta gargajiyar kasar Sin, wato bikin gargajiya na al’ummar Sinawa da ake gudanarwa domin girmama mamata da tunawa da magabata, inda a yau din adadin masu share kaburbura a duk fadin kasar ya yi matukar karuwa fiye da jiya.
Kamar yadda ma’aikatar harkokin jama’a ta kasar Sin ta bayyana, a yau sassan ba da hidimomin jana’iza kimanin 66,200 sun tallafa wajen bayar da hidimomin share kaburbura, baya ga ma’aikata 446,000 da suka shiga ayyukan ba da tabbaci a fannin. A dai yau din, an karbi masu share kaburbura sama da miliyan 30 a fadin kasar, kuma wannan adadin ya karu da kashi 59 da wani abu cikin dari, idan aka kwatanta da na jiya. Cikin adadin, wadanda suka zabi hanyoyin share kaburbura irin na rage gurbatar iska, kamar amfani da furanni sun kai kusan miliyan 20, wanda ya wuce kashi 63 cikin dari na adadin masu share kaburburan. Har ila yau, dandamali 859 na share kaburbura ta yanar gizo sun ba da hidima ga mutane 353,800.
Hukumomin lura da harkokin jama’a, da na ba da hidimar jana’iza a wurare daban-daban, sun tabbatar da dukkan matakan ba da hidima sosai, kana sun gudanar da ayyukan saukaka wa jama’a da amfanin jama’a, don jagorantar jama’a wajen zaben hanyoyin share kaburbura irin na rage gurbata iska. (Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link