UBEC Ta Kaddamar Da Tsarin Dala Miliyan 552 Domin Ilimin Bai-daya

[ad_1]

Ma’aikatar ilimi ta tarayya tare da hadin gwiwar hukumar ilimin bai daya (UBEC) da kuma Shugabannin hukumomin ilimi na Jihohi (SUBEBs), sun kaddamar da tsarin ilimi mai taken HOPE- EDU wanda za a kashe dala milyan 552.18, wanda wani taimako ne ko tallafi domin a samu bunkasa ilimin bai daya da kuma kara inganta ci gaban koyo da koyarwa a kowane sako da lungu na Nijeriya.

Wannan tsari na ilimi tare da gudunmawa daga Bankin Duniya da kuma tsarin hadin gwiwa kan ilimi na duniya (GPE),ana sa ran fiye da yara milyan 29 za su amfana, za kuma a bunkasa ilimin Malaman makaranta 500,000,za a samar da sabbin azuzuwa 13,000,a kuma sake maida milyoyin yara wadanda suka bar makaranta su ma, su koma makaranta domin a koya ma su kamar yadda ake koyawa kowa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *