Yadda jigon APC daga Kano ya rasu a Otel a Abuja

[ad_1]



Wani babban jigo a Jam’iyyar APC daga Jihar Kano, Barista Abdulsalami Ginsau, ya riga mu gidan gaskiya a otel Chida da ke Birnin Tarayya, Abuja.

Marigayi Ginsau, wanda lauya ne kuma Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar a matakin jiha, ya tafi Abuja ne, domin gudanar da aikin tantance masauki ga wakilan jam’iyyar da za su halarci babban taron APC na ƙasa.

Ya isa birnin ne da wuri inda ya duƙufa wajen tanadar ɗakunan kwanan wakilan kafin shi ma ya sauka a otel ɗin Chida.

Lamarin ya auku ne lokacin da aka nemi jigon aka rasa yayin gudanar da taron jam’iyyar a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris.

Abokan aikinsa sun bazama nemansa a sassa daban-daban na Abuja, har ma suka kai rahoton ɓatansa ga hukumar ’yan sanda.

Daga bisani ne jami’an tsaro suka sanar da su cewa an samu wani akasi a otel ɗin da yake zaune, inda aka gano gawar wani mutum.

Bayan abokan aikin nasa sun isa otel ɗinne, suka tabbatar da cewa lallai gawar ta Barista Ginsau ce.

Shugabannin jam’iyyar na zargin cewa rasuwarsa na da alaƙa da lalacewar mahayar otel ɗin.

Wasu daga cikin wakilan jam’iyyar sun riga sun bayyana ƙorafin cewa na’urar mahayar ba ta aiki yadda ya kamata.

Wata majiya daga otel ɗin ta bayyana cewa otel ɗin ya cika maƙil da baƙi, domin sama da mutum 1,000 ne suka sauka a otel ɗin alhali ɗakuna 150 ne kawai aka tanada, lamarin da ya jefa kayan aikin otel ɗin cikin mawuyacin hali.

Majiyar ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin na’urorin mahayar ya samu matsala har ta kai ga an buɗe ta da ƙarfi.

Ana zargin cewa Ginsau, wanda ke zaune a hawa na uku, ya shiga mahayar ne da safe, inda na’urar ta rufe da shi ta kuma faɗa ƙasa da shi ba tare da ma’aikatan otel ɗin sun sani ba.

Sai washegari ne, bayan an fara jin wari yana tashi daga ƙasa aka gudanar da bincike inda aka gano gawar mutum.

Hukumar ’yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce tuni aka fara gudanar da bincike.

Haka kuma, an gudanar da gwajin gawa domin gano musabbabin mutuwarsa.

A nasu ɓangaren, jam’iyyar APC da iyalan marigayin sun buƙaci lallai a binciki gaskiyar lamarin, inda suka bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi da ya girgiza su, musamman ganin cewa ya tafi Abuja cikin ƙoshin lafiya.

Za a gudanar da jana’izarsa a Jihar Kano bisa koyarwar addinin Musulunci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *