Rikici ya sake tashi a Jos bayan sassauta dokar hana fita
[ad_1]
Tashin hankali ya sake barkewa a garin Jos, Jihar Filato, a ranar Laraba bayan sassauta dokar hana fita na awanni 48 da gwamnatin jihar ta kafa a ranar Lahadi.
Barkewar rikicin ya tilasta wa mazauna gari, dalibai da ’yan kasuwa da suka fito bayan sassautar dokar hana fita sun rika gudu don tsira da rayukansu.
A safiyar Laraba, bayan sassautar dokar hana fita, rahotanni sun ce wasu matasa sun kai hare-hare ga direbobi da masu tafiya a ƙafa a sassa daban-daban na garin Jos, abin da ya haifar da tsoro da firgici.
An ce matasa sun toshe hanyoyi zuwa wasu unguwanni, inda aka kashe wasu mutane. A Nasarawa Gwom Junction, mazauna yankin sun rika jifan juna da duwatsu, yayin da direbobi suka yi asarar gilashin motocinsu.
Rahoton ya ce wuraren da abin ya fi shafa sun haɗa da Jami’ar Jos, Bauchi Road, Farin Gada, Tina Junction da Chobe, abin da ya tilasta bankuna da shaguna rufe ayyukansu.
Rahotanni na nuni da cewa dokar hana fitar an kafa ta ne bayan harin da ’yan bindiga suka kai Anguwan Rukuba, inda aka kashe akalla mutane 28 tare da jikkata wasu da dama.
Sai dai gwamnatin jihar ta sassauta dokar bayan samun ɗan sauƙin tsaro.
Kwamishinar Yaɗa Labarai, Joyce Ramnap, ta bayyana a cikin sanarwa cewa daga ranar 1 ga Afrilu, 2026, dokar hana fita za ta kasance daga ƙarfe 7 na safe zuwa 3 na rana, domin ba wa jama’a damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Martanin jama’a
Wata mai shagon kayan abinci a Terminus Market, Joy Bature, ta ce: “Muna tsoron buɗe shagunanmu saboda ba mu san abin da zai iya faruwa ba. Gwamna ya yi kokari wajen sassauta dokar hana fita, amma abin takaici wasu sun ɗauki doka a hannunsu. Gwamnati ta ƙara tabbatar da tsaronmu.”
Kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Jos ta bayyana damuwa kan barazanar da ke fuskantar dalibai da ma’aikata. Shugaban ƙungiyar na duniya, Gad Peter Shamaki, ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara tsaro a dukkan harabar jami’ar, gidajen dalibai da manyan hanyoyin shiga.
“Muna buƙatar sintiri na kowane lokaci, sa ido ta hanyar leƙen asiri, da gaggawar kai dauki domin kare rayukan dalibai da ma’aikata,” in ji shi.
Wasu mazauna yankin sun yi kira da a ƙara tsaro musamman a kusa da Students’ Village Hostel na Jami’ar Jos.
Wani mazaunin Jos, Ishaku Mark, ya ce: “Abin da ake buƙata shi ne jama’a su ci gaba da zaman lafiya, ba ƙara tayar da hankali ba. Dole ne a zakulo waɗanda suka haddasa wannan tashin hankali a hukunta su.”
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai samu damar yin bayani ba. Sai dai majiyoyi daga hedikwatar ’yan sandan jihar sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun shiga wuraren da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya.
Rahoton ya ce sojoji da ’yan sanda sun fara sintiri a manyan hanyoyi, tare da tsayawa a wuraren da ake ganin barazana domin hana sake kai hare-hare.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link