’Yan bindiga sun yi garkuwa da masu aikin gawayi 8 a Filato




’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum takwas masu aikin gawayi a yankin Nyalun da ke shiyyar Bashar a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.

A ranar Talata da dare ne maharan suka yi garkuwa da masu sana’ar gawayin su goma amma daga bisani aka sako biyu daga cikinsu.

Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan sojoji da ’yan banga 20 sun mutu bayan barkewar rikici a tsakaninsu a yankin Wanka da ke shiyyar Keram a Karamar Hukumar Kanam da ke Jihar.

Shugaban matasa na Wase, Shapi’i Sambo, ya shaida wa manema labarai cewa a farko ’yan bindigar sun sace mutane 10 da ke cikin motar, amma daga baya suka saki biyu a yankin Garga, Karamar Hukumar Kanam, domin su sanar da iyalansu su biya kudin fansa.

“Mutanen suna dawowa gida tsakanin ƙarfe 6 zuwa 7 na yamma aka tare motarsu mai ɗauke da gawayi, suka tafi da su. Abin takaici ne domin waɗannan mutane suna ƙoƙarin neman abin dogaro da kansu ne lokacin da lamarin ya faru,” in ji Sambo.

Ya bayyana sunayen waɗanda aka sace da: Hassan Sa’idu, Shamsudden Abubakar, Usamatu Yakubu, Dayyabu Usman Waziri, Inkilulu Dauda, Ado Sambo, Sule Dahiru da Umar Amadu.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka saki, Mummuni Musa, ya ce, “Bayan sun sace mu, sai suka daure mu sannan daga baya suka saki mutane biyu. Sun ce mu koma gida mu faɗa wa mai motar ya sayar da ita ya biya kudin fansar sauran takwas din.”

Rahoton ya nuna cewa ƙauyuka da dama a Wase da Kanam sun dade suna fama da hare-haren ’yan bindiga da satar mutane, wanda ya yi sanadin mutuwar jama’a da dama ciki har da jami’an tsaro, tare da lalata dukiyoyi.

Sakamakon haka, gwamnati ta tura sojoji a ’yan makonnin da suka gabata domin yaƙi da ’yan bindiga a yankin.

Sai dai lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayoyin da suka shafi lamarin ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *