Wani matashi ya kashe matarsa da adda
[ad_1]
Wani matashi mai suna Malime Sunday Ejor, daga ƙauyen Nwang, ya kashe matarsa mai suna Moshie Lucy Igu yayin da suka je gona a ƙauyen Ekajuk ranar Litinin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba, ASP Sunday Eitokpah, ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa: “Wanda ake zargi ya tafi da matarsa ne zuwa gona. Bayan sun tashi daga aikin gona, sai ta ce su je su watsa ruwa a jikinsu kafin su koma gida.
“Suka gangara bakin wani tafki da ke kusa da gidajen mutanen ƙauyen domin yin wanka. Daga nan ne aka ga ta faɗi cikin tafkin. Babu wani motsin mutane a wurin da zai iya ceto ta.
“Wanda ake zargi ya fara saranta da adda da ya tafi da ita gona, yana saranta kamar ana yanka naman dabba, har sai da ta mutu. Daga nan ya bar ta,” inji kakakin ’yan sandan.
Shi dai wanda ake zargi da kisan, yanzu haka an kama shi kuma yana hannun sashen binciken masu aikata miyagun laifuka na rundunar ’yan sanda (SCID), domin bincike kan lamarin.
Ganin irin wannan kisan kai da aka yi wa matar, nan da nan mutanen ƙauyen suka shiga tashin hankali suna shirin ɗaukar fansa. Sai dai jami’an tsaro sun shigo domin kwantar da hankalin jama’a.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link