Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Kungiyar Kula Da Data Ta Duniya

[ad_1]

A yau Litinin ne shugaban Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga kungiyar kula da data ta duniya kan kafuwarta. A cikin wasikar, Xi ya bayyana cewa a halin yanzu, duniya tana shiga wani zamani na fasaha cikin sauri, kuma rawar da bayanai ke takawa a matsayin tushen albarkatu, da injin kirkire-kirkire yana kara bayyana.

Kungiyar kula da data ta duniya, wadda manufarta ita ce “Kawar da gibin bayanai, habaka darajar bayanai, da bunkasa tattalin arzikin dijital,” tana samar da dandali mai muhimmanci na zurfafa hadin gwiwar kasashen duniya kan bayanai, da inganta gudanar da bayanai a duniya.

Xi ya jaddada cewa, Sin za ta rungumi ra’ayin yin shawarwari tare, da bayar da gudummawa tare, da kuma raba fa’idodi tare, kuma za ta goyi bayan rawar da kungiyar kula da data ta duniya za ta taka, da aiki tare da dukkan bangarori wajen gina yarjejeniya kan dokokin gudanar da bayanai, da inganta kirkire-kirkire na fasahar zamani, da inganta gudanar da harkokin tsaro, da ingantaccen ci gaba da amfani da bayanai, da kuma samar da ci gaba mai kyau ga tattalin arzikin dijital na duniya, da kuma ba da damar raba bayanai don amfanin al’ummun dukkan kasashe. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *