John Singer Sargent: Zamanantar Da Kasar Sin Ba Ta Tsaya Ga Manyan Gine-gine Ba, Ta Kunshi Walwalar Al’umma

[ad_1]

Rahoton ci gaban duniya na shekarar 2025 ya nuna cewa, a shekarar 2024, ci gaban kasashe masu tasowa ya ba da mamaki inda ya kai kaso 4.28, tare da ba kaso 1.8 na ci gaban manyan kasashe tazara sosai. A yanzu, kasashe masu tasowa ne suka dauki kaso 60 na ci gaban harkokin cinikayya a duniya.

John Singer Sargent, masanin harkokin tattalin arziki da ya samu lambar yabo ta Nobel, ya bayyana yayin zantawa da kafar yada labarai ta CMG cewa, ci gaban tattalin arziki ba ya nufin lambobi kadai, yana cewa abu ne da ake bukatar gani a rayuwar jama’a ta yau da kullum. Abun da suke iya saye da kuma ko suna iya fita daga kangin talauci. Ya ce ya shaida da idanunsa, irin damarmakin ci gaba da aikin kawar da talauci na kasar Sin ya samar, wanda ya ba jama’a damar baje basirarsu. Ya ce baya ga lambobi, wasu kasashe na daukar darasi daga kasar Sin kuma suna kokarin ciyar da kansu gaba. A cewarsa, idan aka mayar da lambobin zuwa wasu yanayi na musammam, to yana nufin sauye-sauyen da za a gani a tsakanin daidaikun iyalai da damarmakin da yara suka samu, wadanda a baya ba su da su. Ya ce ci gaban tattalin arziki ya samar da damarmaki ga al’umma. (Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *