ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya
[ad_1]
Jam’iyyar ADC ta fara sayar da fom din takara ga masu sha’awar tsayawa takarar mukami a zaben gundumomi da kananan hukumomi da na jihohi da kuma na kasa kafn babban taronta na kasa.
ADC ta gayyaci mambobin jam’iyyar masu sha’awa su sayan fom din takarar a kowace mukami a a cikin jam’iyyar.
- Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani
- Idan Ana Fatan Cimma Nasara A Matakin Kasa Da Kasa, Wajibi Ne A Zabi Kasar Sin
A cikin wata sanarwa da sakataren tsare-tsare na jam’iyya, Pa Idigo, ya sanya hannu, kuma aka raba ta hanyar D a ranar Lahadi. Sai dai kuma farashin fom din ya bambanta bisa matsayi.
A matakin gunduma, farashin fom din shi ne, naira 2,000, yayin da kudaden fom na shugaban gunduma ya tsaya a naira 10,000, sannan sakataren gunduma zai sayi fom din kan naira 5,000 da kuma naira 3,000 don sauran jami’an gunduma.
A matakin kananan hukumomi, farashin fom din shugaban karamar hukuma naira 40,000 ne, sakataren karamar hukuma naira 30,000, kuma sauran jami’an kananan hukumomi naira 10,000 kowanne.
Ga mukaman matakin jiha, fom din shugaban jiha naira 500,000 ne, sakataren jiha naira 300,000 ne, sauran jami’an jiha naira 50,000 kowane daya.
A babban taron jam’iyyar a matakin kasa kuwa, kudin fon din naira 10,000 ga kowane wakili, inda kowace karamar hukuma ke bukatar tura wakili guda daya.
Sanrwar ta kara da cewa kowane mai nema dole ne ya samu adadin masu ba da shawara da ake bukata, kuma kowane mai ba da shawara dole ne ya biya kudi na naira 50.
‘Yan takarar shugaban gundumomi dole su sami masu ba da shawara 10, yayin da sauran jami’an gundumoni suke bukatar biyar kowanne.
A matakin kananan hukumomi, ana bukatar masu neman shugabanci guda 20 da suka rarrabu a duk fadin karamar hukuma, sannan sauran jami’an karamar hukuma ana bukatar samun 10 kowannensu.
Dole ne ‘yan takarar shugabanci a jihohi su samu masu ba da shawara 50 daga ko’ina cikin jihar, tare da akalla daya daga kowanne karamar hukuma, yayin da sauran jami’an jihar ke bukatar masu ba da shawara 20 kowanne.
“Sayarwa da mika fom din ga masu sha’awar tsayawa takara za su fara ne a ranar Jumma’a, 27 ga Maris 2026. Ba za a karbi kowanne fom ba bayan cikar wa’adi.
“An tsara tantancewa daga 30 zuwa 31 ga Maris 2026. Ana ba duk masu neman shiga shawarwarin da su bi wadannan ka’idojin da aka sanya a jaddawalin babban taron jam’iyyar,” sanarwar ta kara da cewa.
[ad_2]
Source link