Matsin Tattalin Arziki: Wani Magidanci Ya Rataye Kansa A Jihar Adamawa

[ad_1]

Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan rasuwar wani mutum mai shekaru 46 da aka samu a rataye a kan itace a Karamar Hukumar Girei ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana mamacin a matsayin Ahmed Mohammed, mazaunin Anguwan Hona, Girei.

  • An Nemi Tinubu Ya Taka Wa Gwamna Bago Birki A Kan Cin Zarafin Kafafen Yada Labaru
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Kaucewa Takara Mai Hadari

Ya ce an gano gawar a kasan Dutse Bagale a ranar Lahadi, sannan aka kai shi Asibitin Cottage na Girei, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

A cewar sanarwar, “Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta samu rahoton rasuwa ta gaggawa da ba ta al’ada ba a ranar 23 ga Maris, 2026, bayan an gano gawar mutum a rataye a kan itace a kasan Dutse Bagale, Karamar Hukumar Girei. Mamacin, Ahmed Mohammed, namiji, mai shekaru 46, mazaunin Unguwar Hona, an kai shi Asibitin Cottage, Girei, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

“Bincike yana ci gaba don gano dalilan da suka haddasa rasuwar,” in ji sanarwar.

‘Yansanda sun yi kira ga ‘yan kasa da ke da bayani mai amfani da su taimaka wajen gudanar da binciken.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *