ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin biyan sabon albashi

[ad_1]



Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki huɗu ta fara biyan sabon tsarin albashi da aka amince da shi ga malaman jami’o’i a faɗin ƙasar.

Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Jihar Bauchi.

Ya ce ƙungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki huɗu daga ranar da ya yi jawabin domin ta fara aiwatar da biyan sabon tsarin albashin, wanda aka amince da shi bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin ɓangarorin biyu.

A cewarsa, idan gwamnati ta gaza aiwatar da hakan cikin wa’adin da aka bayar, ƙungiyar za ta ɗauki mataki mai tsauri.

Piwuna ya ƙara da cewa buƙatar na daga cikin ƙoƙarin da ASUU ke yi na inganta walwalar malaman jami’o’i.

Ya bayyana damuwar cewa ƙarancin albashi na daga cikin abubuwan da ke haddasa ficewar ƙwararrun malamai zuwa ƙasashen waje da kuma taɓarɓarewar tsarin ilimi mai zurfi a Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa duk da yarjejeniyoyi da dama da aka cimma a baya tsakanin ASUU da gwamnati, sau da dama ana samun jinkiri ko rashin aiwatar da su yadda ya kamata, abin da ke haddasa rikice-rikice da yajin aikin jami’o’i.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *