Ministan Wajen Sin Ya Nemi Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Natsuwa Da Warware Sabani Ta Hanyar Tattaunawa
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa Sin na goyon bayan kasashen Gabas ta Tsakiya wajen ci gaba da kasancewa cikin natsuwa da kuma warware sabani da magance rikice-rikice ta hanyar tattaunawa.
Wang, wanda har ila yau memba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, ya yi wannan kira ne a jiya Laraba yayin wata tattaunawa ta waya da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan, bisa bukatar hakan da ministan ya gabatar.
Da yake nuni da cewa a halin yanzu rikicin na yaduwa cikin sauri a fadin yankin, Wang ya ce babban abin da ya fi muhimmanci shi ne karfafa tattaunawar zaman lafiya, da amfani da duk wata dama ta sulhu, da yayyafa ruwa ga wutar rikicin.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan kasashen yankin su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa, su kuma tunkari halin da ake ciki bisa hikima ta hanyar la’akari da muhimman muradunsu na hangen nesa.
Har ila yau duk dai a jiya Laraba, Wang Yi ya tattauna ta waya da ministan harkokin wajen kasar Masar Badr Abdelatty, bisa bukatar hakan da ministan ya gabatar.
Wang ya ce halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya na sauyawa cikin sauri, inda duka Amurka da Iran ke nuna kudurinsu na tattaunawa. Ya jaddada cewa matukar za a tattauna, akwai fatan samun zaman lafiya. Ya kuma ce ya kamata matakan kwamitin sulhun MDD su taimaka ne wajen kashe wutar rikicin da karfafa tattaunawa tare da riga-kafin bazuwar yakin, maimakon amincewa da amfani da karfin tuwo. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link