Griezmann Zai Bar Athletico Madrid A Karshen Kakar Wasa Ta Bana
[ad_1]
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Athletico Madrid Antoine Griezmann zai bar kungiyar ta kasar Sifaniya zuwa kungiyar Orlando City dake buga gasar MLS ta kasar Amurka a karshen kakar wasa ta bana kamar yadda kungiyoyin biyu suka sanar a ranar Talata.
Dan wasan wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin Atletico Madrid ya amince da yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu da Orlando, inda tsohon dan wasan na Barcelona da Real Sociedad zai koma Arewacin Amurka da taka leda, dan wasan gaban zai tafi Orlando a cikin kwanakin hutun da kungiyar ta baiwa yan wasan domin kammala yarjejeniyarsa da kungiyar ta Florida,” in ji Atletico a cikin sanarwar.
Griezmann mai shekaru 35 na fatan kammala kakar wasanshi ta 10 tareda Athletico Madrid tareda lashe kofi a bana, Kofi na karshe da dan wasan na kasar Faransan ya lashe tareda da kungiyar shine na Europa League a shekarar 2018, Griezmann ya lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 tare da Faransa, amma ya yi ritaya daga bugawa kasar kwallo a shekarar 2024 bayan ya zura kwallaye 44 a wasanni 137 da ya buga wa Les Bleus.
Griezmann ya koma Atletico a shekarar 2014 daga Real Sociedad kuma ya buga wasanni 488 a kungiyar, wanda ya bar ta zuwa Barcelona a shekarar 2019 kafin ya dawo shekaru biyu bayan haka, da farko a matsayin aro kafin su kammala sayenshi, a tsawon shekarun da ya shafe a kungiyar ya zura kwallaye 211 a Atletico, inda ya zarce tarihin da Luis Aragones ya kafa a baya na kwallaye 173.
[ad_2]
Source link