Tsohon hadimin Ganduje, Salihu Yakasai, ya koma ADC




Tsohon mai bai wa tsohon gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya sanar da sauya sheƙa daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa ADC (African Democratic Congress).

Yakasai ya bayyana hakan ne a shafukansa na sada zumunta ranar Litinin, inda ya bayyana matakin a matsayin “sabuwar tafiya” a harkokin siyasarsa.

Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tuntubar ‘yan uwa da abokai da kuma abokan hulɗarsa na siyasa, yana mai ƙara da cewa ya riga ya miƙa wa APC takardar murabus ɗinsa sannan ya kammala rajista a sabuwar jam’iyyarsa ta ADC.

“Bayan tuntuɓar ’yan uwa da abokai da abokan siyasa, mun yanke shawarar shiga ADC. Wannan sabuwar tafiya ce, kuma na riga na miƙa wa APC takardar murabus ɗina kuma har na yi rajista a ADC,” in ji shi.

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PRP a Zaɓen 2023 ya kuma ƙarfafa wa magoya bayansa da su yi rajista a jam’iyyar ADC, yana mai cewa ana iya samun katin zama ɗan jam’iyyar cikin sauƙi ta yanar gizo.

Da yake addu’a, Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu ya bayyana fatan cewa jam’iyyar za ta samu nasara wajen kafa gwamnati a faɗin ƙasar nan domin kawo ci gaba ga ‘yan Najeriya.

Yakasai ya taɓa ficewa daga APC a baya bayan an dakatar da shi daga muƙaminsa a 2021, sakamakon sukar da ya yi wa gwamnatin tarayya kan matsalar tsaro a zamanin tsohon shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari.

Daga bisani ya koma PRP inda ya tsaya takarar gwamna a 2023, kafin ya sake koma APC.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *