’Yan bindiga sun sace masu ibada a coci a Kwara
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari wata coci lokacin da ake tsaka da ibada a Jihar Kwara, inda suka sace mutane da dama.
Lamarin ya faru ne a cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke ƙauyen Omugo a Ƙaramar Hukumar Ifelodun.
Shaidu sun ce maharan sun shiga cocin sannan suka fara harbe-harbe, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici, inda kowa ya riƙa gudu domin tsira.
Aƙalla masu ibada takwas suka sace.
Sai dai daga baya uku daga cikinsu sun samu nasarar tserewa, yayin da biyar ke hannun maharan har yanzu.
Gwamnatin Jihar Kwara ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana shi a matsayin abin damuwa.
Ta yaba wa jami’an tsaro, masu gadin dazuka da kuma ’yan sa-kai bisa saurin kai ɗauki da suka yi, wanda ya taimaka wajen kuɓutar da wasu daga cikin mutanen.
Gwamnatin ta kuma buƙaci a ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda ke tsare da kuma cafke masu laifin.
Haka kuma ta roƙi jama’a da hukumomin tsaro su ci gaba da haɗa kai domin yaƙi da laifuka a yankin, tare da jaddada ƙudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link