Isra’ila ta hana Sallar Idi a Masallacin Qudus karo na farko cikin shekaru 59

[ad_1]



A karon farko cikin shekaru 59, ba a ji kiran sallah ba a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Jerusalem, bayan da hukumomin Isra’ila suka hana masu ibada gudanar da Sallar Eid al-Fitr.

Rahotanni sun ce babu kowa a harabar masallacin, lamarin da ya saɓa wa yadda dubban masu ibada ke cika shi a irin wannan lokaci na ƙarshen watan Ramadan.

Matakin ya biyo bayan rufe masallacin mai daɗɗeɗen tarihi a birnin Jerusalem tun daga ranar 28 ga Fabrairu, inda hukumomi suka danganta hakan da yanayin dokar ta-ɓaci sakamakon yaƙin da ke gudana tsakanin Iran da ƙawancen Amurka da Isra’ila.

Rufewar dai ta shafi muhimman lokutan ibada na Musulmi kamar Juma’ar ƙarshe ta Ramadan da kuma Sallar Idin, haɗi da kwanaki goma na ƙarshen watan mai falala.

Falasɗinawa sun bayyana damuwa kan hana su shiga masallacin, wanda shi ne al-Qibla ta farko a Musulunci, suna mai cewa an tauye musu ’yancin addini.

Haka kuma, matakin ya shafi Kiristoci, inda aka dakatar da ibadu a Church of the Holy Sepulchre, ciki har da bukukuwan Easter, wanda ake sa ran dubban masu ibada za su halarta.

Wannan lamari ya kawo cikas mai girma ga al’ummomin Musulmi da Kirista a Jerusalem, inda aka hana su gudanar da muhimman ibadunsu na shekara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *