Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri

[ad_1]



Wata mata mai aikin shara da goge-goge, Fa’iza Abdulkadir, ta mayar da kuɗi har N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusun bankinta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Da take zantawa da News Central a Maiduguri, Fa’iza wadda take ɗaukan albashin Naira dubu 30 duk wata ta ce ta yanke shawarar mayar da kuɗin ne saboda tsoron Allah.

“Wannan kuɗi ba haƙƙi na ba ne, ba ni na mallaki kuɗin ba, shi ya sa na mayar. Na fi son na zauna cikin kwanciyar hankali da kuma gudun azabar Allah a ranar lahira,” in ji ta.

Fa’iza ta bayyana cewa ta shafe kwanaki uku tana zaraya a banki kafin ta kammala duk matakan mayar da kuɗin.

“Na shafe kwanaki uku babu sukuni don ko abincin kirki ba na samu na ci yadda kamata har sai da na mayar da kuɗin, sannan na samu kwanciyar hankali,” in ji ta.

Ma’aikatan banki da maƙwabta a unguwar da take zaune sun bayyana Fa’iza a matsayin mace mai gaskiya wadda take rayuwa da albashin N30,000 da take samu daga wata cibiyar lafiya inda take aiki.

“Ba abin mamaki ba ne, saboda yadda take da tarbiyya da kuma yadda take renon ‘ya’yanta.

“Tana da kyawawan ɗabi’u, kuma tana rayuwa cikin rufin asiri da ‘ya’yanta guda biyar,” in ji wata maƙwabciyarta.

Wani jami’in banki ya ce abin da Fa’iza ta yi ya ba mutane mamaki sosai. “Duk da halin da take ciki, ta ji tsoron Allah ta yi abin da ya dace.

“Na taɓa ganin irin haka ta faru a wannan banki inda aka yi kuskuren tura kuɗi a asusun wani, ya cire kuɗin ya kashe.

“Sai da ya jefa ma’aikatan banki cikin tashin hankali don hatta ‘yan sanda sun shiga lamarin, amma har yanzu ba a dawo da kuɗin ba,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *