Ban yi nadamar abubuwan da na yi lokacin da nake minista ba — Malami

[ad_1]



Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce bai yi nadama kan duk abin da ya yi lokacin da yake riƙe da muƙami ba.

Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya kare kansa a gaban kotu kan tuhumar da ake masa.

Ana tuhumar Malami tare da matarsa Asabe da ɗansa Abdulaziz da laifuka guda 16 da suka shafi zargin almundahanar kuɗi.

Hukumar EFCC cw ta gurfanar da su a gaban kotu kan tuhume-tuhumen, sai dai dukkaninsu sun musanta zarge-zargen.

A wata hira da ya yi, Malami ya ce zamansa a tsare a hannun EFCC, da zaman gidan yarin Kuje, da kuma hannun DSS, wani ɓangare ne na rayuwarsa.

Ya ce yana ganin komai yana cikin nufin Allah, amma duk da haka zai kare kansa a kotu.

Idan ba a manta ba kotu ta bayar sa belinsa, amma daga bisani jami’an DSS suka sake kama shi a ranar 19 ga watan Janairu.

Ya kuma koka cewa ba a ba shi damar ganin iyalansa da lauyoyinsa ba yayin da yake tsare.

A ranar 27 ga watan Fabrairu, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da belinsa shi da ɗansa kan kuɗi Naira miliyan 200 kowannensu kan wasu zarge-zarge daban.

Sun cika sharuɗan belin kuma yanzu haka an sake su.

Malami, ya kuma zargi hukumomin tsaro da take masa haƙƙinsa.

Ya ce sun binciki gidajensa da wuraren kasuwancinsa ba tare da sanar da shi ba, wanda ya ce hakan ya saɓa da doka.

Duk da wannan shari’a da ake yi, Malami ya jaddada cewa yana tsaye kan ra’ayinsa a kan duk abin da ya yi a lokacin da yake minista, kuma bai yi wata nadama ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *