Sin Ta Samun Gaggarumin Ci Gaban Ayyukan Taimakon Masu Bukata Ta Musamman
[ad_1]
Kwanan nan, aka rufe gasar wasannin Olympics ta masu bukata ta musamman ta lokacin hunturu karo na 14 a Italiya. Tawagar ‘yan wasa ta Sin ta samu lambobin yabo 44, ciki har da zinare 15, azurfa 13 da tagulla 16 a gasar, lamarin da ya sa ta zo ta farko a wajen yawan cin lambobin zinare da kuma lambobin yabo gaba daya, kuma hakan ya zama mafi kyawun sakamako a tarihin kasar wajen halartar gasar da aka shirya a ketare. Yayin da aka daga tutar kasar Sin sau da dama a wajen gasar, nasarorin da ‘yan wasan masu bukata ta musamman na Sin suka samu ba wai kawai nasarori na wasanni ba ne, a maimakon haka, shaida ce na bunkasar ayyukan taimakon masu bukata ta musamman a Sin. Daga wannan bangare, muna iya ganin yadda ake ta inganta ayyukan tabbatar da rayuwar masu bukata ta musamman da yawansu ya kai miliyan 85 a nan kasar Sin.
Ta fannin tabbatar da rayuwar masu bukata ta musamman, ya zuwa watan Yuni na shekara ta 2025, kimanin masu bukata ta musamman da ke cikin wahala miliyan 11 da dubu 884 na samun tallafin kudade daga gwamnatin Sin, kuma yawan masu bukata ta musamman da ke fama da tsananin nakasa da suke samun tallafin kudi na musamman ya kai miliyan 16.4. Har wa yau, yawan masu bukata ta musamman da suka shiga inshorar ritaya ga mazauna birane da karkara da inshorar kiwon lafiya ya kai kashi 90% da kuma 95%. Wadannan alkaluma sun shaida cewa, Sin tana da ingantaccen tsari na ba da tabbaci ga rayuwar masu bukata ta musamman.
Ilimi shi ne mabudi ga masu bukata ta musamman don su cimma darajar rayuwarsu. A cikin shekaru biyar da suka gabata (2021-2025), adadin yara masu bukata ta musamman da suka shiga makaranta a matakin ilimin tilas na shekaru 9 ya karu zuwa kashi 97%. Sai kuma a bangaren aikin yi, adadin masu bukata ta musamman da ke da aikin yi a fadin kasar ya kai miliyan 9.01, kuma karin masu bukata ta musamman da suka samu guraben aikin yi a birane da karkara ya wuce miliyan 2.31. A halin yanzu ana aiwatar da “shirin aiki na shekaru uku don inganta samar da aikin yi ga masu bukata ta musamman (2025-2027)” , kuma ana ci gaba da yi wa tsarin aikin yi ga masu bukata ta musamman na Sin kwaskwarima ta yadda za a samar musu aikin yi mai kyau da inganci.
Kimiyya da fasaha na taimaka wa masu bukata ta musamman wajen cimma burinsu. Daga fasahar hada kwakwalwa da na’ura da na’urori masu tallafa wa masu bukata ta musamman, zuwa hannayen mutum-mutumi masu sarrafa kansu, ana gaggauta amfani da fasahohin zamani wajen amfanar masu bukata ta musamman a yau da kullum.
An rubuta nasarorin da ‘yan wasa masu bukata ta musamman na kasar Sin suka cimma a kundin tarihi, sai dai abin lura shi ne: sama da kashi 90% na masu bukata ta musamman a kasar suna samun tabbacin rayuwarsu, kuma masu bukata ta musamman miliyan 9.01 suna da aikin yi, baya ga kashi 97% na yara masu bukata ta musamman a kasar sun samu damar shiga makaranta, har ma ra’ayin tallafa wa masu bukata ta musamman ya yadu daga birane zuwa karkara, daga kayan aiki zuwa manhajoji. A nan Sin, kowane mai bukata ta musamman yana da damar cimma nasara dogaro da karfinsa!(Mai zane da rubutu: MINA)
[ad_2]
Source link