Sarkin Musulmi Ya Ba Da Umarnin Fara Duban Jinjirin Watan Shawwal Ranar Laraba
[ad_1]
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi a faɗin Nijeriya da su fara duban jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan 1447 bayan hijira da kuma fara bukukuwan Sallah ƙarama.
A cikin wata sanarwa da Majalisar Masarautar Sakkwato ta fitar, an bayyana cewa ranar Laraba, 18 ga watan Maris, 2026 (wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan), ita ce ranar da za a duba jinjirin watan.
- CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025
- Tinubu Ya Bai Wa Masu Riƙe Da Muƙamai Da Ke Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus
Ya buƙaci Musulmi su duba jinjirin watan da yamma, sannan su kai rahoto ta hanyoyin da aka tanada.
Duk wanda ya ga jinjirin watan ya sanar da hakimin unguwarsa ko ƙauyensa, wanda zai isar da saƙonn ga Sarkin Musulmi domin tabbatarwa da sanarwa a hukumance.
Haka kuma, majalisar ta samar da lambobin waya domin sauƙaƙa isar da rahoton ganin watan.
A addinin Musulunci, ganin jinjirin watan Shawwal ne ke nuna ƙarshen azumin Ramadan da kuma fara bikin Sallah, ɗaya daga cikin manyan bukukuwan da Musulmi ke yi duk shekara.
[ad_2]
Source link