Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane Da Dama, Ciki Har Da Ƴan Jarida
[ad_1]
Rahotanni daga Gaza sun tabbatar da cewa an kashe ƴan jarida huɗu a wani mummunan hari da aka kai kan asibitin Nasser, ciki har da Mohammed Salama na Al Jazeera, Hossam al-Masri na Reuters, Moaz Abu Taha na NBC, da kuma Mariam Abu Daqa na Associated Press. Wannan ya ɗaga adadin ƴan jaridar da aka kashe tun bayan fara rikicin zuwa a ƙalla 244.
Hare-haren, wanda Isra’ila ta bayyana a matsayin “sumamen ƙarshe” don mamaye dukkan yankin Gaza, ya ƙara tsananta halin da ake ciki a lokacin da yunwa ta yi ƙamari a yankin. Likitoci sun bayyana cewa babu isassun kayan agaji ko abinci don ceto rayukan yaran da ke fama da tsananin yunwa.
Shaidu sun bayyana cewa jirgin sama marar matuƙi ne ya fara luguden wuta kan ginin asibitin a safiyar yau, lamarin da ya haifar da girgiza mai tsanani a cikin yankin.
A cewar rahotanni, mutane 14 ne suka rasa rayukansu nan take a harin, ciki har da ƴan jarida huɗu, wani jami’in agaji, da kuma fararen hula goma, lamarin da ya ƙara dagula rayuwar al’ummar Gaza da ke ci gaba da fuskantar hare-hare da tsanantawar yunwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link