Kungiyar Nazarin Ci Gaban Hakkokin Dan Adam Ta Kasar Sin Ta Kira Taro Mai Taken “Kawar Da Rashin Adalci Don Neman Samun Hakkin Ci Gaba” A Geneva
[ad_1]
A yayin taro na 61 na majalisar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHRC), kungiyar nazarin ci gaban hakkokin dan Adam ta kasar Sin ta kira wani taro mai lakabin “kawar da rashin adalci don neman samun hakkin ci gaba” a ranar 13 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda kwararru da masana na kasar Sin da na sauran kasashe suka tattauna kan yadda za a bai wa kowane dan Adam hakkin ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkiren dabaru, yayin da duniyarmu ke fuskantar matsaloli da dama da suka shafi tattalin arziki da zaman rayuwar dan Adam da muhalli da sauransu.
Mahalarta taron sun ce, bai wa kowane dan Adam hakkin ci gaba shi ne muhimmin ginshikin samun hakkin ci gaba na dan Adam. Shawarar samar da ci gaba ga duk duniya da kasar Sin ta gabatar, mai kunshe da ka’idar amfanar da kowa tare da nuna hakuri, ta kara zurfafa ma’anar akidar tabbatar da adalci wajen samun hakkin ci gaba. Taron ya kuma yi kira ga sassan kasa da kasa, su inganta hadin gwiwa, da kawar da rashin adalci a bangaren tsari, da kokarin raya tsarin jagorancin duniya mai adalci da kuma dorewa. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link