Isra’ila ta ce ta kashe manyan jami’an leƙen asirin Iran biyu a Tehran

[ad_1]

Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe wasu manyan jami’an leƙen asirin Iran biyu a wani hari da suka kai a birnin Tehran, babban birnin ƙasar.

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa mutanen da aka kashe sun haɗa da Abdollah Jalali-Nasab da kuma Amir Shariat, waɗanda suka kasance manyan jami’ai a sashen leƙen asiri na rundunar Khatam al-Anbiya, wadda ke kula da manyan ayyukan sojin Iran.

A cewar Isra’ila, an kashe jami’an ne a ranar Juma’a, kwanaki kaɗan bayan an naɗa su domin maye gurbin tsohon shugaban sashen leƙen asirin rundunar, Saleh Asadi, wanda aka kashe a farkon yaƙin.

Rahoton ya ce Asadi ya mutu ne a ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da Isra’ila tare da Amurka suka ƙaddamar da hare-hare na farko a wani farmaki da aka kira Operation Roaring Lion.

Sojojin Isra’ila sun ce sashen leƙen asirin na rundunar Khatam al-Anbiya na da alhakin tattarawa da nazarin bayanan sirri, wanda yake gabatar wa manyan shugabannin tsaron Iran domin yanke shawara kan yaƙin da suke yi da Isra’ila.

Isra’ila ta kuma ce wasu manyan jami’an gwamnatin Iran da dama sun mutu a tun a jerin hare-haren da suka ƙaddamar a ƙarshen watan Fabrairu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *