Manyan Kamfanonin Sin Suna Zuba Karin Jari A Jihar Xinjiang Ta Kasar
[ad_1]
A jiya Juma’a, kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati, na majalisar gudanarwar kasar Sin, da gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar, suka gabatar da alkaluman zuba jari da manyan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin suka samar a jihar ta Xinjiang, cikin shekaru 5 da suka gabata.
Alkaluman sun nuna cewa, a shekarar 2025 kadai, manyan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin sun zuba jarin da yawansa ya kai Yuan biliyan 265.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 38.5 a jihar Xinjiang, tare da samar da guraben aikin yi dubu 107 a jihar. Ban da haka, kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin, sun zuba jarin kudi da ya kai dala biliyan 159.5 a jihar Xinjiang, cikin shekaru 5 da suka gabata, lamarin da ya kasance babban taimako ga jihar, a kokarinta na raya tattalin arziki da zaman al’umma.
Haka zalika, duk a jiya Juma’a, wasu manyan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin 18, sun kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa da gwamnatin jihar Xinjiang, na neman kaddamar da sabbin ayyuka 92, wadanda suka shafi bangarorin makamashi, da sarrafa ma’adinai, da samar da na’urorin aiki na zamani, da dai sauransu.
A cewar darektan kwamitin sanya ido kan kadarorin mallakar gwamnati na majalisar gudanarwar kasar Sin, Zhang Yuzhuo, ana zuba karin jari a jihar Xinjiang ne domin neman damar samar da guraben aikin yi, da damar wadatar da kai ga jama’ar wurin, da karfafa cudanya tsakanin mutane ‘yan kabilu daban daban, tare da ba da cikakkiyar kulawa ga dukkan al’ummun jihar ta Xinjiang. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link