Rikice-rikicen Da Suka Addabi PDP Ne Suka Sa Na Koma APC — Gwamnan Zamfara

[ad_1]

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma shari’o’in da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ne suka sa ya fice daga jam’iyyar ya koma APC.

A ranar Litinin ne gwamnan ya sanar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance.

  • Ramadan: ‘Yansanda Sun Buƙaci A Sanya Ido A Kano A Goman Ƙarshe
  • APC Na Da Gwamnoni 31 Bayan Sauya Sheƙar Gwamnan Zamfara

Hakan ya faru ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne domin muradun al’ummar Zamfara.

Sanarwar ta ƙara da cewa an yanke shawarar komawa APC ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar, musamman ganin matsalolin shari’a da jam’iyyar PDP ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamna Dauda Lawal ya ce ya yi ƙoƙari sosai domin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarorin PDP, domin a samu haɗin kai kuma jam’iyyar ta samu damar tsayar da ‘yan takara a zaɓuka masu zuwa.

Sai dai ya ce duk ƙoƙarin da aka yi na sasanci bai yi nasara ba.

Wannan ne ya jawo yawaitar shari’o’i da ka iya kawo cikas ga ‘yan siyasa da ke shirin tsayawa takara a zaɓen 2027.

Ficewar Dauda Lawal daga PDP na zuwa ne mako guda bayan gwamnan Adamawa ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

A yanzu haka PDP na da gwamnoni biyu kacal, yayin da APC ke da gwamnoni 31 a faɗin ƙasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *