Yaƙin Amurka Da Iran Na Iya Tura Farashin Litar Fetur Zuwa N2,000 A Nijeriya – PETROAN
[ad_1]
Ƙungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta yi gargaɗin cewa farashin litar fetur a Nijeriya na iya kaiwa kusan ₦2,000 idan rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya ci gaba da dagula samar da man fetur a duniya.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Billy Gillis-Harry, ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Fatakwal, inda ya gabatar da jawabi kan batun tsaron makamashi. Ya ce yaƙin da ya haɗa da Israel, Amurka da Iran na tura farashin mai a kasuwar duniya sama.
- Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Rage Farashin Mai Zuwa ₦774
- Matatar Dangote Ta Sake Ƙara Farashin Fetur Zuwa ₦1,175
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na PETROAN, Joseph Obele, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da makamai masu linzami a yankin na barazana ga manyan hanyoyin jigilar mai da muhimman kayayyakin mai, abin da ke haifar da rashin tabbas a kasuwar duniya.
Ƙungiyar ta ce kafin rikicin, ana sayar da fetur kusan N774 a lita, amma yanzu farashin ya haura N1,000, wanda ya nuna ƙarin kusan kashi 30 cikin ɗari. Haka kuma farashin dizal ya tashi daga kusan N950 zuwa sama da N1,400 a lita.
Shugaban PETROAN ya ƙara da cewa idan rikicin ya ci gaba, farashin fetur na iya kusantar N2,000 a lita, yayin da dizal kuma zai iya kai kusan N3,000, lamarin da zai ƙara tsananta matsin tattalin arziƙin ga ‘yan kasuwa da al’umma a Nijeriya.
[ad_2]
Source link