Darussa Daga Ramadan Na 16: Amfani Da Dama Kafin Ta Wuce
[ad_1]
A cikin watan Ramalana muna koyon darasi mai girma, watau amfani da dama kafin ta kuɓuce. Domin dama idan ta shuɗe, ba lallai ta dawo da irin yanayinta ba. Lokaci kamar gajimare ne, yana wucewa ba tare da tsayawa ba.
Allah Maɗaukaki Ya tuna mana da ƙimar lokaci a cikin ayoyin azumi, inda Ya ce a cikin Suratul Baƙara aya ta (184): “Waɗansu kwanaki ne ƙididdigaggu” Watau Ramalana ba wata ba ne mai dawwama; kwanaki ne kaɗan, masu ƙidaya, masu iyaka. Wannan kalma ta ‘ƙididdigaggu’ tana tunasar da mu cewa duk wata dama da Allah Ya ba mu tana da iyaka. Idan muka yi sakaci da ita, za ta shuɗe kamar ba ta taɓa zuwa ba.
- Darussa Daga Ramadan Na 14: Yawaita Kyauta Da Ihsani A Ramalana
- Darussa Daga Ramadan Na 13: Tsayuwar Dare
Ramalana yana koya mana yadda za mu daraja lokaci. Yana koya mana cewa yini guda na iya zama hanyar samun gafara, dare guda na iya zama sanadin tsira, kuma awa guda na iya sauya makomar rayuwa.
Idan muka san cewa kwanakin Ramalana ƙalilan ne, za mu yi ƙoƙari mu cika su da alheri. Za mu nisanci ɓata lokaci a kan abin da ba ya amfanar da mu. Za mu fahimci cewa jinkiri da sakaci su ne manyan maƙiyan nasara.
Wannan darasi bai tsaya a kan Ramalana kaɗai ba. Rayuwarmu gaba ɗaya ‘kwanaki ne ƙididdigaggu’ Shekaru suna wucewa, ƙuruciya tana gushewa, ƙarfi yana raguwa. Duk wanda ya fahimci haka, to zai yi gaggawar cika rayuwarsa da ayyukan da za su amfane shi a duniya da Lahira.
Ramalana wata dama ce ta sabunta rayuwa. Idan muka iya amfani da kwanakin nan yadda ya kamata, za su zama hujja a gare mu, ba hujja a kanmu ba. Saboda haka, mu riƙe kowace rana a matsayin baiwa a gare mu. Mu riƙe kowane dare a matsayin wata dama ce babba a tare da mu. Kada mu bari lokutanmu su tafi a iska. Domin idan dama ta wuce, ba za ta dawo da irin darajarta ba.
Allah Ya taimake mu wajen amfani da lokutanmu cikin abin da zai amfane mu, Ya sa kwanakinmu su zama masu albarka, Ya kuma ba mu kyakkyawan ƙarshe. Amin.
[ad_2]
Source link