Shettima Ya Yi Alƙawarin Zafafa  Yaƙi Da Ta’addanci A Arewa-Maso-Gabas


Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi alƙawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta kawo ƙarshen ta’addanci a yankin Arewa-Maso-Gabas ta hanyar “karfafa ƙarfin Soji,” biyo bayan wasu hare-hare masu muni da aka kai a Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar ta hannun Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Kafofin Watsa Labarai, Stanley Nkwocha, Shettima ya ce gwamnati ba za ta bar fargaba ta sanya ta dakatar da aiki ba, duk da satar mutane a Ngoshe da hare-haren da aka kai kan rundunonin Soja.

  • Tinubu Ya Tura Kashim Shettima Kano, Ya Yi Alƙawarin Tallafin Kuɗi Ga Ƴan Kasuwar Singa
  • 2027: Tinubu Ya Jaddada Shirin Tafiyarsa Tare Da Shettima

“Muna ɗaya daga kasa cikin ƙasashe da suke fama matsalar tsaro. Mutuncin rayuwar ɗan adam ba abin sassauci ba ne. Wannan rashin imanin da suke zai kawo ƙarshe, ba da magana kawai ba, amma da ƙarfin hukuma,” in ji shi.

Shettima ya bayyana cewa ana ƙara tura kayan aiki na dabaru da ƙarin Sojoji bisa bayanan sirri zuwa wuraren da abin ya shafa. Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya samu rahoto kan lamarin kuma ya umarci “ayi gaggawar tura dukkanin matakan samar da tsaro.”

Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta lamunci barin wata mafaka ga waɗanda ke neman tilasta wa mutane barin gidajensu ko mamaye wani wuri a Nijeriya ba. Shettima ya yi alƙawarin cewa waɗanda suka aikata laifukan za su fuskanci hukunci bisa doka, sannan waɗanda aka sace za a mayar da su gida cikin aminci ga iyalansu.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya yi godiya ga jajircewar mazauna Jihar Borno ƙarƙashin gwamna Babagana Zulum da kuma jaruntakar Sojojin da ke fagen daga. Shugaba Bola Tinubu kuma ya nuna tausayawa da goyon baya ga gwamnan yayin da ya kira shi kan hare-haren, yana mai tabbatarwa cewa Nijeriya za ta ci gaba da samun nasara kan ta’addanci.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *