Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Cimma Nasarar Manufar Nan Ta Inganta Lafiyar Jama’a A Wa’adin Shirin Raya Kasa Karo Na 15
[ad_1]
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a kara azamar cimma nasarar manufar nan ta inganta lafiyar jama’a mai halayyar musamman ta Sin, domin ingiza ci gaban tsarin kiwon lafiyar al’umma, cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 wato tsakanin shekarar 2026 zuwa 2030.
Xi Jinping ya yi kiran ne a Juma’ar nan, yayin da ya halarci zaman wakilai mahalarta taro na 4, na majalisar bayar da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14.
Kazalika, shugaba Xi ya kuma gabatar da sakon gaisuwa da fatan alheri ga daukacin matan kasar Sin na dukkanin kabilu, daga dukkanin sassan rayuwa, gabanin bikin ranar mata ta duniya da za a yi bikinta a ranar takwas ga watan nan na Maris. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link